<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>114</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Halleluya! Halleluya! Halleluya!
 Wahalarka, Mai Fansarmu,
 Ta kawo ceto dominmu,
 Ta buɗe rijiyar rai yanzu, Halleluya!

[V2]
 2) Aikin Shaiɗan da gurinsa,
 Ka ƃata su da giciyenka,
 Ka ba da rai domin mu rayu, Halleluya!

[V3]
 3) Kai ne kaɗai mai nasara
 Kan Shaiɗan duk da ƴaƴansa,
 Ka kā da su da ikonka, Halleluya!

[V4]
 4) Kai ne ka jawo mu wurinka,
 Kai ne ka kawo gafara,
 Kai ne ka ba mu Ruhunka, Halleluya!

[V5]
 5) Kai ne ka gama cetonmu,
 Ka hau can Sama dominmu,
 Kai ne mai zuwa dominmu, Halleluya!

[V6]
 6) Yabo ga Allah sai mu yi,
 Yabo ga Yesu, Masu Bi,
 Yabo ga Ruhu Mai Tsarki, Halleluya!</lyrics>
<title>Halleluya! Halleluya! Halleluya! Wahalarka LW114</title>
</song>